Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Khatibzade ya kara da cewa: “dole ne kasar Amurka ta cire dukkan takunkumin da ta kakaba mata a lokacin guda, tare kuma da bada aminci na cewa tarihi ba zai maimaita kansa ba.
Iran tana da karfin guiwa da kyakkyawar niya na shiga tattaunawar da za’a yi a Biyanna da kuma zimmar ganin an cire dukkan takunkumin zalunci da aka kakabawa Al’ummar kasar .
Labarin da jaridar Newyork times ta wallafa ya nuna cewa me yi wu wa Amurka ta yi tayin sakin wasu kadarorin Iran da aka toshe , da kuma dauke mata wasu haramcin da aka sanya mata, daura da haka ita kuma za ta jingine wasu ayyukan ta na nukiliya.
342/